logo

HAUSA

Manzon musamman na shugaban kasar Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban Afrika ta Kudu

2024-06-17 19:50:37 CMG Hausa

Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Xiao Jie, zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, wanda za a yi ranar 19 ga wata a birnin Pretoria.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ne ya sanar da haka a yau Litinin, yayin taron manema labarai na kulla-yaumin.

A cewar kakakin, gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ce ta gayyaci Xiao Jie, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, kakakin ya bayyana imanin cewa, sabuwar gwamnatin kasar Afrika ta Kudu, za ta jagoranci al’ummar kasar wajen cimma nasarori a kan hanyarta ta gina kasa. Haka kuma, kasar Sin na daukar batun raya dangantakar dake tsakaninta da Afrika ta Kudu da muhimmanci, kuma a shirye take ta hada hannu da sabuwar gwamnatin wajen inganta aminci da juna a fannin siyasa da fadada hadin gwiwarsu a aikace da karfafa hadin gwiwa kan manyan tsare-tsare a duniya da ma shiyya shiyya, da kuma inganta gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da Afrika ta Kudu. (Fa’iza Mustapha)