Me Ya Sa Kamfanonin Waje Ke Neman Ci Gaba A Kasar Sin
2024-06-17 21:59:55 CMG Hausa
Yau Litinin, kasar Sin ta fitar da yadda aka tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar a watan Mayu, wanda ya nuna cewa, gaba daya tattalin arzikin kasar yana tafiya yadda ya kamata, tare da sake farfado da wasu muhimman bangarori, wadanda suke ci gaba da inganta, ta yadda har suke karfafa gwiwar kamfanonin kasashen waje, wajen ci gaba da gudanar da cinikayya a kasar.
Wannan ci gaba ya samo asali ne daga babbar kasuwar kasar Sin, kuma dalilin da ya sa kasuwar kasar Sin ke jan hankali shi ne, ana samun saurin bunkasuwa ta fuskar yin kirkire-kirkire.
A ganin kamfanonin kasashen waje masu yawa, fifikon da kasar Sin ke da shi a fagen kwararru da fasahohi, da ma yawan masu sayayya, da cikakken tsarin samar da kayayyaki, ya sanya kuzari ga yin kirkire-kirkire. A saboda haka ne suka zabi yin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin don kiyaye karfinsu na yin takara a duniya.
Bisa karuwar karfin yin kirkire-kirkire, da zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka, da kuma cimma burin bunkasuwa a shekarar da muke ciki. Ko shakka babu, irin wannan kasar Sin ta zama “zabi na dole” ga kamfanonin kasashen waje da yawa. (Bilkisu Xin)