logo

HAUSA

Li Qiang ya gana da manyan jami’an kasar Austriliya

2024-06-17 10:23:22 CMG Hausa

Da safiyar yau Litinin ne firaministan kasar Sin Li Qiang wanda ke ziyarar aiki a Canberra, fadar mulkin kasar Australiya, ya gana da shugaban majalisar dattawa Sue Lines da na wakilai Milton Dick na kasar Austriliya.

A ganawarsu, Li Qiang ya ce, huldar dake tsakanin kasashen biyu ta koma hanya da ta dace bayan da ta yi fama da rikici a shekarun baya, wannan ba abu mai sauki ba. Ya kamata bangarorin biyu su yi iyakacin kokari cikin yakini don samun karin ci gaba, kuma hakan na matukar bukatar rawar da hukumomin kafa doka da shari’a na kasashen biyu za su taka. Yana mai fatan majalisar dokokin Austriliya da ta goyi bayan sahihan matakan da bangarorin biyu za su dauka da samar da tabbaci a bangaren doka da siyasa.

A cewarsa, Sin da Austriliya na da mabambantan tarihi da tsarin al’umma, shi ya sa suke fuskantar bambancin ra’ayi kan wasu batutuwa, abin da a sa gaba shi ne kara tuntubar juna don kara fahimtar juna da kawar da shakku. Gwamnatin Sin na goyon bayan hukumomin dokokin bangarorin biyu da su kara yin mu’ammala da maraba da mambobin majalisar Austrilya da su kai ziyarar a kasar Sin don ganewa idanunsu sauye-sauyen da Sin ta yi, ta yadda za su kara fahimtar juna.

A nasu bangare, Sue Lines da Milton Dick sun bayyana farin cikinsu na ganin huldar kasashen biyu na tafiya yadda ya kamata. Majalisarsu na fatan kara tuntubar bangaren Sin don ingiza ci gaban huldarsu, wanda zai amfanar da al’umommin kasashen biyu. (Amina Xu)