logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da wasikar murnar cika shekaru 100 da kafa kwalejin soja ta Huangpu da bikin cika shekaru 40 da kafa kungiyar tsofaffin daliban kwalejin soja ta Huangpu

2024-06-17 21:09:45 CMG Hausa

Gabannin bikin cika shekaru 100 da kafa kwalejin soja ta Huangpu, da kuma cika shekaru 40 da kafa kungiyar tsofaffin daliban kwalejin soja ta Huangpu, sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasa, kuma shugaban kwamitin soja na tsakiyar kasar Xi Jinping, ya aike da wasika a madadin kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar, domin taya kungiyar tsoffin daliban kwalejin soja ta Huangpu murna.

A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, kwalejin soja ta Huangpu ta samo asali ne daga hadin gwiwar farko tsakanin jam’iyyar Kuomintang da jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma ita ce makaranta ta farko a kasar Sin da ta horar da jami’an sojan juyin juya hali. Ya ce kungiyar tsofaffin daliban kwalejin soja ta Huangpu, kungiya ce mai kishin kasa karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin, wadda ta hada daliban Huangpu da danginsu dake ciki da wajen kasar Sin. Ya kara da cewa, tun daga lokacin da aka kafa ta, ta ba da babbar gudummawa ga fadada mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, da yaki da balle Taiwan daga yankin kasar Sin, da kuma dinkewar kasar Sin baki daya.

Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan sabuwar tafiya, ya kamata kungiyar tsofaffin daliban kwalejin soja ta Huangpu ta kiyaye manufar kafa ta, da nauyin dake wuyanta ta fuskar siyasa, da kuma ci gaba da inganta ruhin Huangpu na "kishin kasa da juyin juya hali", kana da tsayawa tsayin daka kan yaki da balle Taiwan daga yankin kasar Sin, da inganta dinkewar kasar Sin, da ma karfafa hadin gwiwa kan cimma babban burin kasar baki daya. (Bilkisu Xin)