logo

HAUSA

Sanarwar taron kolin G7 ta yi amfani da batutuwan da suka shafi kasar Sin wajen shafa mata bakin fenti

2024-06-17 19:56:52 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, sanarwar taron kolin G7 ta sake kara gishiri kan batutuwan da suka shafi kasar Sin, don shafawa kasar bakin fenti da kai mata hari.

Lin Jian ya bayyana haka ne a yau Litinin, a gun taron manema labaru da aka saba yi a kullum.

Rahotanni sun ce, taron kolin G7 ya fitar da wata sanarwa, inda aka tattauna halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, tare da yin tsokaci maras tushe kan batutuwan da suka shafi tekun gabashin kasar Sin, tekun kudancin kasar Sin, da Hong Kong, da Xinjiang, da Xizang, da dai sauransu, da kuma kara gishiri kan batun, wai yawan kayayyakin da masana’antun kasar suka samar ya wuce kima.

Game da haka, jami’in ya bayyana cewa, sanarwar taron koli na G7 na cike da girman kai, son zuciya, da karairayi, wadda ta kara amfani da tsoffin batutuwan da ba su da tushe, kuma ba sa bisa doron doka, da duk wani zance na dabi'a.

Baya ga haka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, ma’aikatar tsaron Amurka ta kaddamar da wani kamfen na yada labarai ta yanar gizo a asirce kan kasar Sin yayin barkewar cutar numfashi ta COVID-19, wato ta hanyar kafa asusun karya don yin rubutu a shafukan sada zumunta, da nufin zargin aminci da ingancin allurar riga kafi ta Sci Tech ta kasar Sin.

Game da hakan, kakakin ya bayyana cewa, lamarin dai ya sha tabbatar da cewa, a ko da yaushe Amurka na amfani da kafafen sada zumunta wajen yada labaran karya, da gurbata muhallin ra’ayin jama’a, da kuma bata sunan wasu kasashe, wadanda kasar Sin ke adawa da su. (Bilkisu Xin)