Mutane sun gudanar da zanga-zangar adawa da G7
2024-06-16 16:31:51 CMG Hausa
Da yammacin ranar rufe taron kolin G7 a jiya Asabar, dimbin masu zanga-zanga sun taru a birnin Fasano da ke yankin kudancin Italiya, inda aka gudanar da taron, domin gudanar da zanga-zangar adawa da kungiyar.
Dubban masu zanga-zangar sun yi ta ruri tare da daga allunan nuna adawa da yaki, don yin Allah wadai da ayyukan kungiyar G7 na kafa “kananan kungiyoyi” da kara tsananta rikici da kuma rura wutar adawa a rikicin Rasha da Ukraine.
Masu zanga-zangar sun kuma ce kungiyar G7 ta yi ikirarin taimakawa kasashe masu tasowa wajen tunkarar sauyin yanayi da kuma rage basussukan “kasashen kudancin duniya”, wanda suka bayyana a matsayin yunkuri mai kyau da ya gaza samuwa. Kana sun jaddada bukatar yaki da manufofin da ba na kasuwa ba, wadanda ke lalata yanayin gasa mai adalci da tsaron tattalin arziki, inda suke zargin kasashen G7 da kasancewa kan gaba wajen tsunduma cikin kariyar ciniki da kuma yin watsi da ka'idojin gudanar da cinikayya cikin ‘yanci. (Bilkisu Xin)