Shugaban tarayyar Najeriya ya taya al`ummar kasar murnar salla
2024-06-16 17:29:22 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin al`ummar musulmin kasar murnar bikin babbar salla.
Sakon na shugaban kasa yana kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban Mr. Ajure Ngelale wadda kuma aka rabawa manema labarai jiya Asabar 15 ga wata a birnin Abuja,ya ce bikin salla bai tsaya kawai kan shagulgulaba ba kadai .
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Sanarwar ta ambato shugaban na tarayyar Najeriya na cewa bukukuwan musulunci irin wannan yana karawa al`ummar tausayin juna da hadin kai a tsakani, kana da nuna godiya ga Allah bisa koshin lafiyar da ya baiwa bayinsa har suka sheda bikin da yake zuwa a duk shekara.
Shugaban na tarayyar Najeriya har ila yau ya ce jajircewa tare da sadaukar da kai manya sinadarai ne da suke taimakawa kasa ta ginu, a don haka ya nemi al`ummar Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na bikin babbar salla wajen hada kai domin kawo canji mai ma`ana ga harkokin cigaban kasa, har ila yau kuma ya bukaci addu’o’in cigaba da wanzuwar zaman lafiya a kasa baki daya.
Tun a ranar Juma`ar da ta gabata ne dai gwamnatin tarayya ta sanar da kebe ranakun Litinin 17 ga wata da kuma Talata 18 a matsayin ranar hutu domin baiwa al`umma damar gudanar da shagulgulan bikin babbar sallah. (Garba Abdullahi Bagwai)