Yau ne al`ummar musulmi a Najeriya suka bi sahun na sauran kasashe wajen bikin babbar sallah
2024-06-16 19:52:35 CMG Hausa
Yau Lahadi 16 ga wata daidai da 10 ga watan Zhulhijja, musulmi a Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen gudanar da idin babbar sallah.
Tuni dai mutanen da suke da halin suka gudanar da layyar su kamar yadda addinin musulunci ya shara`anta ga mai iko.
Sai dai duk da matsin tattalin arziki da al`ummar kasar ke fuskanta na hauhawar farashin kayayyaki da karyewar darajar kudin kasar, amma rahotannin sun tabbatar da cewa an gudanar da hawan idin cikin kwanciyar hankali a dukkan biranen kasar.
Wakilin mu dake tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya zantawa da wasu daga cikin al`ummomi inda suka bayyana farin cikinsu bisa yadda suka sheda ranar sallar cikin koshin lafiya tare da addu`ar Allah ya sake zaunar da kasar lafiya.
Daga bisani kuma sun isar da sakonsu na barka da sallah ga `yan uwa da abokan arzuka.
“Suna na Amina Abdullahi daga garin Kano, ina yi wa `yan uwa da abokan arziki barka da salla da fatan kowa ya yi salla lafiya musamman kanwa ta Hafsa da kuma `ya ta Safna, sannan kuma ina kara mika sakon barka da salla ga `yan uwa na da suke garin Sakkwato, sannan ina mika sakon gaisuwa da jinjina ga ma`aikatan gidan rediyon kasar Sin muna yi masu fatan alheri”
“Suna na Aishatu Badamasi Ahmad daga garin Kano ina yi wa daukacin al’ummar musulmin duniya barka da babbar salla musamman kanwa ta Maryam da Asiya da kuma Umma na da kuma Ahmad, Aminu Badamasi da kuma Hanif da Hanifa ina fatan sun yi salla lafiya, kuma jinjina da fatan alheri ga ma`aikatan gidan rediyon kasar Sin da fatan sun yi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ta badin badin badada”
“Suna na Najib Sulaiman daga jihar Kanon Najeriya ina yiwa al`ummar jihar Kano da kafatanin al`ummar Najeriya da na Afirka gaba daya barka da salla, ina yi wa Yusuf Sulaiman Ahmad da mai gidana Husaini daga jihar Katsina barka da sallah.”
“Suna na Yakubu Babangida Umar daga jihar Kanon Najeriya, ina yi wa dimbun al`ummar duniya barka da salla da fatan anyi salla lafiya, sai kuma al`ummar jihar Taraba ina yi wa Shamil Isa daga Jalingo kasar Muri ina mishi barka da sallah da fatan ya yi salla lafiya.”(Garba Abdullahi Bagwai)