Hadin gwiwar Sin da Australia zai ketare tekun Pasifik da zarce bambance bambance
2024-06-16 17:20:01 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce muddin bangarorin biyu za su raya dangantakarsu, hadin gwiwa tsakanin Sin da Australia zai iya ketare fadin tekun Pasifik, ya zarce bambance-bambance da cimma nasarori da sakamakon moriyar juna.
Li Qiang ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci gidan adana dabbobi na hadin gwiwar Sin da Australia na Adelaide, game da bincike da kare dabbobin Panda.
Yayin rangadin, Li Qiang ya ce gidan adana dabbobin masauki ne ga Wang Wang da Fu Ni, dabbobin Panda biyu kacal dake akwai a kudancin duniya, kuma duk da sun yi nisa daga gida, ana kula da su sosai, kana sun samu mazauni, inda su ke rayuwa cikin farin ciki a Australia.
An yi aron Wang Wang da Fu Ni ne tun a shekarar 2009, kuma suna daga cikin abubuwa mafiya jan hankali a gidan dabbobi na Adelaide. Bisa yajejeniyar dake tsakanin bangarorin biyu, a bana ne za su dawo gida.
Li Qiang ya kara da cewa, dabbobin sun zama jakadun dangantakar Sin da Australia kuma alama ta muhimmiyar abota tsakanin al’ummomin biyu.
Ya ce a shirye Sin take ta ci gaba da hadin gwiwa da Australia kan bayar da kariya da bincike game da dabbobin Panda, kuma da fatan Australia za ta ci gaba da kasancewa gida ga dabbobin. (Fa’iza Mustapha)