Ya kamata Amurka ta cire Cuba daga jerin "kasashe masu goyon bayan ta'addanci"
2024-06-16 17:15:44 CMG Hausa
Kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu da “G77 da Sin” sun fitar da sanarwa cikin hadin gwiwa, inda suka bukaci ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gaggauta cire kasar Cuba daga cikin jerin “kasashe masu goyon bayan ta'addanci”, da kuma soke matakan matsawa al'ummar Cuban.
Sanarwar ta ranar 14 ga wata, ta ce shigar da Cuba cikin jerin "kasashe masu goyon bayan ta'addanci" rashin adalci ne kuma mataki ne maras tushe, inda suka bayyana shi a matsayin yunkurin neman fakewa da sanya karin takunkumi akan Cuba, wanda ya kafa shingen da ba a taba ganin irinsa ba ga tattalin arziki da kasuwanci, da hada-hadar kudi ta al'ummar Cuba.
Kaza lika, sanarwar ta kuma nanata kakkausar adawarta ga aiwatar da matakan matsin lamba dake illata wasu yankuna, ciki har da saka takunkumi kan kasashe masu tasowa. (Bilkisu Xin)