logo

HAUSA

Mataimakin shugaban Brazil: Sin ta nuna babban misali a fannin yaki da fatara da bunkasa fasahohi

2024-06-15 15:20:53 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kasar Brazil Geraldo Alckmin, ya ce kasar Sin ta nuna babban misali a fannin yaki da fatara, da bunkasa dunkulewar sassa daban daban, da raya tattalin arziki da bunkasa fasahohi.

Mista Alckmin, ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da ya yi kwanan nan da ‘yan jaridar kafar CMG ta kasar Sin, lokacin da yake ziyarar aiki a kasar.

Alckmin ya ce Sin ta zamo babban karfi dake ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. Kuma a duk lokacin da kasar ke kara bunkasa da ci gaba, baya ga ita kan ta, sauran sassan duniya ma na amfana daga ci gaban na ta.

Ya ce a shekarun da suka gabata, hadin gwiwa tsakanin Brazil da Sin na ci gaba da yaukaka, kana yana ci gaba da ba da gudummawar samar da guraben ayyukan yi, da karin kudaden shiga, da bunkasa tattalin arzikin al’ummun sassan biyu. Daga nan sai ya yi fatan kasashen biyu za su karfafa ayyukan hukumomin kasa da kasa tare, za su goyi bayan cudanyar sassa daban daban, kana za su yi aiki wajen gina duniya mai adalci, da zaman lafiya, da hadin kai da ci gaba.  (Saminu Alhassan)