Sayayyar motoci a kasar Sin ta karu da kaso 8.3% tsakanin watan Janairu da Mayun bana
2024-06-15 15:00:11 CMG Hausa
Sayayyar motoci a kasuwannin kasar Sin ta karu da kaso 8.3% cikin watanni 5 na farkon shekarar nan ta 2024, idan an kwatanta da jimillar makamancin lokaci na shekarar bara, inda yawan motocin da aka sayar ya kai kimanin miliyan 11.5, bisa alkaluman da hadaddiyar kungiyar kamfanonin kera motoci ta kasar Sin ta gabatar a jiya Juma'a.
An ce ko a watan Mayu kadai, yawan motocin da aka sayar a kasar Sin ya riga ya kai kimanin miliyan 2 da dubu 420, jimillar da ta karu da kaso 1.5% kan na makamancin lokaci na shekarar bara. (Bello Wang)