Jiragen dakon kaya masu zirga zirga tsakanin Sin da Turai sun gudanar da zirga zirga mafi yawa a Mayu
2024-06-15 16:25:24 CMG Hausa
Kamfanin zirga zirgar jiragen kasa ta kasar Sin, ya ce a watan Mayu da ya gabata, jiragen dakon kaya masu zirga zirga tsakanin Sin da Turai, sun gudanar da zirga zirga mafi yawa.
Cikin watan na Mayu, adadin zirga zirgar jiragen ta karu da kaso 14 bisa dari a shekara, inda adadin zirga zirgar ya kai 1,724, yayin da adadin kayan da jiragen suka yi dako, bisa mizanin sundukai masu tsayin kafa 20, ya kai 186,000, karuwar da ta kai ta kaso 13 bisa dari, sama da na shekarar bara. Kamfanin ya ce a watan na Mayu ne aka yi dakon adadin kaya mafi yawa cikin wata guda a duk tarihin sufurin.
Har ila yau, alkaluman kamfanin sun nuna cewa, tun daga farkon shekarar nan, kamfanin jiragen kasa na Sin, ya gaggauta samar da tsare tsaren aikewa da hajoji na zamani, ya tsara sufurin manyan hajoji yadda ya kamata, tare da ci gaba da kyautata ingancin hidimomi, da fadin ayyukan safara ta layin dogo.
A daya bangaren kuma, kamfanin ya ce a watan Mayu, an yi safarar hajoji ta layukan dogon kasar, wadanda yawan su ya kai tan miliyan 337, adadin da ya nuna karuwar kaso 2.8 bisa dari a shekara. Saminu Alhassan)