logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya yi kira da a ci gaba da kyautata huldar dake tsakanin Sin da New Zealand

2024-06-15 14:56:19 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin na son aiki tare da kasar New Zealand, wajen daukaka matsaya daya da suka cimma, da karfafa dankon zumunci, gami da kokarin kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2 mai alaka da manyan tsare-tsare a dukkan fannoni.

Li ya yi furucin ne a jiya Juma'a, lokacin da yake gabatar da wani jawabi a bikin liyafar maraba da zuwa da al’ummun sassa daban daban suka shirya masa, a birnin Auckland na kasar New Zealand, taron da firaministan kasar New Zealand Christopher Luxon shi ma ya halarta.

A cewar Mista Li Qiang, kasar Sin a shirye take ta karfafa cudanya da hadin gwiwa tare da New Zealand, a ayyukan fannoni daban daban, da zummar samar da karin alfanu ga al'ummun kasashen 2, gami da ba da gudunmowa a kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pacific, har ma da dukkanin duniya baki daya.

A nasa bangare, firaministan kasar New Zealand Christopher Luxon, ya ce kasarsa za ta ci gaba da dora babban muhimmanci kan raya huldarta da kasar ta Sin, kana New Zealand na fatan yin aiki tare da kasar Sin, wajen karfafa zumuncin gargajiya, da zurfafa cudanya, da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da ciniki, da aikin gona, da ikon mallakar ilimi, da raya ilimi, da fannin yawon shakatawa, gami da kokarin tinkarar wasu kalubaloli tare, wadanda suka hada da sauyin yanayin duniya, da gurbacewar muhallin halittu. (Bello Wang)