logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya Cyril Ramaphosa murnar sake zama shugaban kasar Afirka ta Kudu

2024-06-15 14:59:01 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya Matamela Cyril Ramaphosa murnar sake zama shugaban kasar Afirka ta Kudu.

A cikin sakon da ya aike a jiya Juma'a, shugaba Xi ya ce, Sin da Afirka ta Kudu suna amincewa da juna a fannin harkokin siyasa, gami da aiwatar da hadin gwiwa a dimbin fannoni, tare da samar da sakamako masu armashi, ta yadda suka zama abin koyi ta fuskar gudanar da hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa. Shugaban na kasar Sin ya ce yana dora matukar muhimmanci kan ci gaban huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Afirka ta Kudu, inda yake son kokarin aiki tare da shugaba Ramaphosa, wajen neman daga huldar dake tsakanin kasashen 2 mai alaka da manyan tsare-tsare a dukkan fannoni zuwa wani sabon matsayi, da samar da gudunmawa ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da walwala a duniya. (Bello Wang)