Firaministan Sin ya isa Australia domin fara ziyarar aiki
2024-06-15 20:52:41 CMG Hausa
A yau Asabar ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa kasar Australia domin fara ziyarar aiki. Yayin da yake kasar, Li tare da takwaransa na Australia Anthony Albanese, za su yi hadin gwiwar jagorantar taron shekara shekara karo na 9, na shugabannin Sin da Australia, kana za su halarci taron tattaunawa na manyan jami’an kasashen biyu. (Saminu Alhassan)