logo

HAUSA

Tawagar MDD ta tsakiyar Sahel ta kawo karshen ziyarar Nijar

2024-06-14 14:11:59 CMG Hausa

Wata babbar tawagar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin tsakiyar Sahel ta kawo karshen ziyarar da ta kai Nijar yau Juma’a, kuma kakakin MDD ya sanar da zuba jarin dalar Amurka miliyan 9.5 a kasar domin inganta samar da makamashi a jamhuriyar Nijar, da nufin karfafa hanyoyin samar da makamashin kasar domin biyan bukatun makamashi mai dorewa kuma mai inganci.

Farhan Haq, mukaddashin kakakin babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce tawagar daraktoci na MDD karkashin jagorancin mataimakin babban sakataren MDD Abdoulaye Mar Dieye, mai kula da harkokin ci gaba na MDD a yankin Sahel, ta kammala zangon farko na ziyarar aiki a tsakiyar Sahel.

Haq ya kara da cewa, tawagar ta kasance a Nijar daga ranar 9 zuwa 13 ga watan Yuni, kuma za ta ziyarci kasar Mali a mako mai zuwa, tare da shirin kai ziyara a Burkina Faso nan gaba. (Yahaya)