logo

HAUSA

Sabuwar wakiliyar UNICEF a Nijar ta kama aiki

2024-06-14 09:44:45 CMG Hausa

Sabuwar wakiliyar kungiyar asusun kula da yara ta MDD a Nijar UNICEF, madam Djanabou Mahande ta kama aiki gadan gadan a ranar jiya Alhamis 13 ga watan Junin shekarar 2024, bayan ta mika takardar wakilcinta ga ministan harkokin wajen kasar Nijar, Bakary Yaou Sangare. Inda, bikin ya gudana a ma’aikatarsa da ke birnin Yamai a gaban mataimakan manyan jami’an biyu.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

’Yar asalin kasar Kamaru, madam Djanabou Mahande na da kwarewar aiki ta kusan shekaru 20, a fannin ci gaba da kula da ayyukan gaggawa a yankin Afrika da kudancin Asiya.

Sabuwar wakiliyar UNICEF a Nijar, kwarrara ce a fannin ilimin zamantakewa, da ’yancin dan Adam, ’yancin kananan yara da matasa, mata da kuma agajin jin kai.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.