logo

HAUSA

Sin da Amurka sun yi tattaunawa na “China–US Track 1.5 Dialogue” karo na 2 a Beijing

2024-06-14 14:44:01 CMG Hausa

 

Jiya Alhamis, hukumar hulda da jam’iyyun siyasar kasashen waje na kwamitin kolin JKS da kungiya mai kula da harkokin Asiya ta Amurka sun yi hadin gwiwar gabatar da tattaunawa da ake kira “China–US Track 1.5 Dialogue” karo na biyu a nan birnin Beijing. Bangarorin biyu sun yi mu’ammala mai zurfi cikin sahihanci tare da cimma matsaya daya bisa taken “Mai da muhimmanci kan abubuwa mafi jawo hankali da ingiza mu’ammala da hadin gwiwa”.

Bangarorin suna ganin cewa, kamata ya yi Sin da Amurka su nace ga zaman tare cikin lumana da kaucewa barkewar rikice-rikice, kana da kara yin mu’ammala da tuntubar juna da ingiza fahimta da amincewa da juna, kazalika da zurfafa hadin gwiwarsu a bangaren tattalin arziki da cinikayya da tinkarar sauyin yanayi da kiwon lafiya da fasahar kwaikwayon dan Adama AI da dai sauransu, har ma da habaka mu’ammalar al’adu musamman ma tsakanin matasa. Dadin dadawa, an kara daidaita kalubaloli da mai da hankali kan magance bambancin ra’ayi, kuma da sauke nauyin dake wuyansu a matsayin kasa masu karfi don tinkarar kalubalolin duniya tare. A cikin tattaunawarsu kuma, sun kai ga matsaya daya na kara zurfafa mu’ammala ta yadda za a taka rawar gani wajen ingiza huldar kasashen biyu mai dorewa yadda ya kamata. (Amina Xu)