Sin: A bara darajar cinikayya tsakanin kasashen shiyya karkashin RCEP ta kai dala triliyan 5.6
2024-06-14 20:56:46 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta Sin He Yadong, ya ce hadaddiyar yarjejeniyar shiyya ta kawance ko RCEP, wadda aka fara aiwatarwa shekara guda da ta gabata, ta ingiza matsayin bude kofa, da hadin gwiwa a shiyyar, tare da kara kyautata kwarin gwiwar bunkasa farfadowar tattalin arzikin duniya.
Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2023, darajar cinikayyar shiyya karkashin RCEP, ta kai dala triliyan 5.6, kana hadin gwiwa tsakanin ayyukan masana’antu, da tsarin samar da hajoji tsakanin yankunan shiyyar ya ci gaba da fadada. A dai shekarar ta bara, darajar sashen zuba jarin kai tsaye a fannonin da ba na hada hadar kudi ba na Sin zuwa sauran kasashe mambobin yarjejeniyar ta RCEP, ya kai dala biliyan 18.06 a shekara, adadin da ya samu karuwar kaso 26 bisa dari.
Kasashe 15 ciki har da Sin, da Japan, da Korea ta kudu, da Australia, da New Zealand, da kasashe 10 mambobin kungiyar ASEAN ne suka kulla yarjejeniyar ta RCEP. (Saminu Alhassan)