logo

HAUSA

Babbar kotun Nijar ta cirewa Mohamed Bazoum rigar kariya

2024-06-14 21:31:33 CMG Hausa

Babbar kotun janhuriyar Nijar ta ba da umarnin cirewa shugaba Mohamed Bazoum, wanda sojoji suka yiwa juyin mulki a bara rigar kariya, kamar dai yadda lauyan sa ya bayyana hakan a Juma’ar nan. Sakamakon hakan, a yanzu mahukuntan kasar na da ikon gabatar da shi gaban kuliya. (Saminu Alhassan)