logo

HAUSA

Sin: Kada hadin gwiwar Philippine da Amurka ya gurgunta tsaro da daidaiton shiyya

2024-06-14 19:17:05 CMG Hausa

Yayin taron manema labarai na yau Juma’a, mataimakin daraktan ofishin watsa labarai na ma’aikatar tsaron kasar Sin, kuma kakakin ma’aikatar kanal Zhang Xiaogang, ya fitar da sako game da wasu batutuwa da suka shafi ayyukan soji, inda game da atisayen tallafawa harkokin sufurin sama na hadin gwiwa tsakanin dakarun sojin kasa na Philippine da na Amurka, Zhang Xiaogang ya ce Sin na fatan hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu, ba zai kai ga haifar da illa ga wani sashe na daban ba, kuma kada ya gurgunta tsaro da daidaiton shiyyar.

Don gane da musun da Philippine ta yi, cewa sojin ta sun nuna bindiga ga jirgin ruwan tsaron teku na Sin ba, Zhang Xiaogang ya ce Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka wajaba, na shawo kan matakai masu hadari da tsagin Philippine ke dada aiwatarwa.

Game da daidaita kasafin kudaden ayyukan soji na shekarar 2025 da Amurka ta aiwatar kuwa, wanda ya kunshi karin kudi har dala biliyan 18, da nufin tunkarar kasar Sin da wasu karin kasashe masu karfi kuwa, Zhang Xiaogang ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gyara kuskurenta yadda ya kamata game da irin kallon da take yiwa kasar Sin, kana ta rungumi manufar dora ci gaban alakar rundunonin sojin kasashen biyu kan turba ta gari. (Saminu Alhassan)