logo

HAUSA

An saki ’yan Nijar biyu da aka kama a tashar Seme-Podji yayin da aka tura uku gidan yari

2024-06-14 09:23:25 CMG Hausa

 

A kasar Benin, ’yan Nijar biyar da aka kama a tashar Seme-Podji sun bayyana a gaban babban alkalin kotun musamman ta CRIET a ranar jiya Alhamis 13 ga watan Junin shekarar 2024. Bayan hukumomin kasar Benin sun ce sun kama su da laifi.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada, ya turo mana da wannan rahoto. 

Wadannan ’yan Nijar guda biyar sun bayyana gaban alkalin kotun yaki da yi ma tattalin arziki zagon kasa da yaki da ta’addanci CRIET, ’yan sandan kasar Benin sun kama su a ranar Laraba 5 ga watan Junin shekarar 2024.

A cewar jaridar Libre Express, madam Aminou Hadiza Ibra, mataimakiyar darektan kamfanin WAPCO-Nijar, da Ismael Cisse Ibrahim, sufeton man fetur, da Mousbahou Dan Kane, sufeton man fetur, da Saidou Harouna Oumarou, injiniyan man fetur, kuma kwararre a kamfanin WAPCO-Nijar sai kuma Abdoul Razak Djibo, injiniya kuma kwararre a kamfanin WAPCO-Niger.

Bayan an saurare su, kotun musamman ta CRIET ta saki biyu daga cikinsu, a cewar kafar rediyon Peace FM. Sauran uku an yanke musu hukuncin zaman yari daga ciki har da mataimakiyar darektan WAPCO-Niger. Ana zarginsu da amfani da katin shaidar ma’aikata ta jabu, kuma za’a sake sauransu a ranar Litinin 17 ga watan Junin shekarar 2024, in ji gidan rediyon Peace FM.

A cewar jaridar, Libre Express, hudu daga cikin ma’aikatan sun iso kotun a ranar jiya da misalin karfe 11 na rana sanya da tufafin kamfanin kasar WAPCO-Niger, da ke kula da bututun mai Niger-Benin.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai, a jamhuriyyar Nijar.