Kasar Sin na amfani da karfin hasken rana don yi wa hanyar mota a yankin hamada ban ruwa
2024-06-14 16:28:35 CMG Hausa
Zuwa ranar Litinin ta wannan makon da muke ciki, aikin babbar hanyar mota dake cikin yankin hamada, mai suna Tarim Desert Highway a turance, wanda shi ne aikin ban ruwa bisa karfin hasken rana kuma mai yaki da kwararar hamada mafi tsawo a kasar Sin, ya samar da wutar lantarki mai karfin kWh miliyan 500 ko fiye, al’amarin dake taimakawa sosai a fannonin yaki da kwararar hamada, gami da kiyaye muhallin halittu a wurin.