Kaso 96.4% na sana’o’in kasuwanci na Sin mallakin sassa masu zaman kan su ne
2024-06-13 20:30:01 CMG Hausa
Ya zuwa karshen watan Mayu da ya shude, adadin sana’o’in kasuwanci mallakin sassa masu zaman kan su a kasar Sin ya kai miliyan 180.45, adadin da ya kai kaso 96.4 bisa dari na daukacin kamfanonin kasar masu gudanar da hada hadar kasuwanci, kamar dai yadda hukumar dake sanya ido kan harkokin kasuwanni ta kasar ta tabbatar.
Wannan adadi a cewar hukumar, ya karu daga kaso 95.5 bisa dari da kasar ke da shi a shekarar 2019. Kaza lika, Sin ta zamo kasa mai adadin kamfanoni masu zaman kan su da yawan su ya kusa miliyan 55.18, da kuma sama da kamfanonin da suka samarwa masu mallakar su ayyukan yi sama da miliyan 125.27. (Saminu Alhassan)