logo

HAUSA

AU na tsara ka’idojin bunkasa amincin abinci a kasuwanni

2024-06-13 10:23:22 CMG Hausa

 

Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) da hadin gwiwar cibiyar binciken dabbobin da ake kiwo a gida (ILRI), dake Nairobin kasar Kenya, sun ce tuni aka fara tsara sabbin ka’idojin bunkasa amincin abinci a kasuwannin da aka kafa ba bisa ka’idojin gwamnati ba. 

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a Nairobi, hukumomin biyu sun ce, sun lura kusan kaso 70 na iyalai a biranen nahiyar, na sayen abinci daga irin wadannan kasuwanni, da suka hada da masu sayar da abinci a bakin titi da kantuna, lamarin dake bukatar tabbatar da ingancinsu domin kare masu sayayya daga gubar abinci.

Jami’in kula da ingancin abinci na hukumar kula da albarkatun dabbobi na AU (AU-IBAR), John Oppong-Otoo ya ce, amincin abinci da abubuwan gina jiki, hakki ne na dan Adam, sai dai abinci mara aminci na keta hakkin miliyoyin ‘yan Afrika a kowacce shekara. Ya ce, sun yi imanin cewa, sabbin ka’idojin za su ba da hakikanin jagorancin da za su taimakawa gwamnatoci hada hannu da bangaren mara ka’ida, da kuma sauya shi zuwa mai aminci da zai iya wadatar da jama’a.

A cewar AU, ana sa ran sabbin ka’idojin za su sanya kuzari ga kokarin da ake yi a kasashe na inganta amincin abinci a Afrika, ta hanyar damawa da masu tsara manufofi da masu saye da sayarwa, a matsayin wani bangare na ajandar nahiyar ta kawo karshen yunwa da fatara da cututtuka.

An fara wallafa ka’idojin, wadanda aka kirkiro bayan shirin AU na tabbatar da amincin abinci a Afrika daga shekarar 2022 zuwa ta 2036, karon farko a shekarar 2021, da nufin bunkasa tabbatar da tsafta yayin tu’amali da kayayyakin abinci.  (Fa’iza Mustapha)