logo

HAUSA

Gasar kwallon kafa ta kauye ko VSL na samar da damar musaya tsakanin al’ummun Sin da na kasa da kasa

2024-06-13 20:11:20 CMG Hausa

A ranar da aka gudanar da bikin ranar yara ta kasa da kasa, tauraron kwallon kafa dan kasar Italiya Fabio Cannavaro, ya ziyarci kasar Sin, inda kai tsaye ya wuce wurin da ake gudanar da gasar kwallon kafa ta kauye, ko “China Village Super League (VSL)”, ya kuma bayyana gamsuwa da yadda mazauna kauyuka ke nuna karsashi, da sha’awar taka leda yadda ya kamata.

Gasar VSL, wadda da harshen Sinanci ake cewa "Cun Chao,", an fara gudanar da ita ne a gundumar Rongjiang ta lardin Guizhou na kudu maso yammacin kasar Sin tun daga shekarar 2023, daga nan ne kuma wasan ya fara yaduwa cikin sauri a sassan kasar Sin, da ma wasu sassan kasashen duniya, saboda irin saukin shirya gasar, da kuma yadda ake hada ta da bukukuwan nuna fasahohin al’adun gargajiya.

A karshen watan Mayun da ya shude ma, tauraron dan kwallon kasar Brazil Kaka, shi ma ya halarci gasar ta VSL, inda har ya buga gasar sada zumunta tare da ‘yan wasan dake buga wannan kwallo a Rongjiang.

A cewar Kaka, "Abu ne mai faranta rai samun damar zuwa nan wurin, inda na samu tarba daga mutane masu son baki, masu son jama’a, kana na hadu da jama’a masu more nishadi tare".

ZIYARAR TAURARIN ‘YAN KWALLO

Yayin da gasar VSL ke kara samun karbuwa, gundumar Rongjiang ta karbi bakuncin miliyoyin masu yawon bude ido, da masu sha’awar kwallon kafa tun daga shekarar 2023 zuwa yanzu. Sai dai kuma, zuwan Kaka ne karon farko da gundumar mai tsaunuka ta karbi bakuncin babban tauraron dan kwallon kafa na kasa da kasa.

Duk da cewa ranar aiki ce, filin wasan kauyen ya cika da masu yawon bude ido da suka halarci wurin domin su hango fitowar Kaka. Yayin da ya fito ta mashigar filin wasan yana murmushi kuwa, ‘yan kallon, da masu buga kwallon sun barke da shewa.

Kaka ya ce gidauniyar kawance ta kasar Sin mai rajin bunkasa zaman lafiya da ci gaba, da wani kamfanin kera wayoyin salula na kasar ne suka gayyace shi, zuwa kallon gasar sada zumunta mai lakabin “Neman cimma muradu, ko "Chasing Dreams" a turance, wadda aka shirya da nufin bunkasa wasan kwallon kafa tsakanin mutanen dake yankin, da ma gasar VSL da ake bugawa a wurin.

Yayin da yake Rongjiang, Kaka ya kalli wasan kwallo da aka buga tsakanin daliban makarantun firamare dake gundumar. Ya kuma ce "A  Brazil, muna taka leda a rairayin bakin teku, muna buga kwallo da abokanan mu, don haka kwallon kafa bangare ne na al’adun mu; Abun da na gani a nan, ya yi kama da na gida. Abu ne mai muhimmanci a yayata kwallon kafa tsakanin matasa, kuma abun da ya kara burge ni shi ne ganin ‘yara mata na buga kwallo, tare da fatan cimma burikan su a  Rongjiang. A gani na kaunar wasan na da muhimmanci, kuma na ga yadda ‘yan mata ke sha’awar wasan. A nawa ra’ayin, abu ne mai kayatarwa zuwa na Sin, tare da zama jakada mai ingiza matasa su shiga wasan kwallon kafa, tare da taimaka musu cimma burikan su masu nasaba da hakan".

A karshen mako, daliban firamare guda 2 daga gundumar Rongjiang, wadanda ke cikin yara mambobin kungiyoyin kwallon kafa masu lakabin “Neman cimma muradu, ko "Chasing Dream", sun samu gayyatar zuwa kallon wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na zakarun turai ko UEFA Champions League, wanda aka buga a filin wasa na Wembley dake birnin London.

Long Tongyi, ‘yar shekaru 10 da haihuwa daga firamaren garin Guzhou, daya ce daga ‘yaran da suka samu gayyatar, ta kuma ce ta fara buga kwallon kafa tun tana aji 3, ta kuma yabawa tauraron kwallon kafa Kaka, wanda ta ce yana da matukar kwarewa ta nuna fasahohin wasan.

Duk da cewa shekara daya kacal ta yi tana buga kwallo, Long ta yi imanin cewa, tana daf da cimma burin ta na zama kwararriyar ‘yar kwallon kafa. A matsayin ta na mace data tilo cikin iyalin gidan su dake yin wasan, ta nunawa iyalin ta nasarar da take samu a fannin karatu, domin tabbatar musu cewa wasan kwallo da take bugawa, ba ya hana ta cimma nasara a bangaren karatu, sabanin dar dar da suke nunawa game da hakan. Long ta ce "Domin samun damar yin atisayen kwallon kafa, ina tashi da sassafe, kana ina yin aikin gwajin lissafi bayan na kammala horon kwallo".

Dong Yongheng, dan wasa ne dake buga gasar VSL, kuma babban masoyin Kaka, ya kuma ce duk da cewa taurarin ‘yan wasan kwallon kafa da dama sun ziyarci inda ake buga Cun Chao cikin kusan shekara guda, a nasa bangare yana cike da shaukin ganin Kaka a garin su. A ganin sa ziyarar Kaka za ta inganta karbuwar VSL, da kara jawo masu sha’awar kwallo zuwa wannan gasar kwallon kafa da ake yi a kauye.

A nasa bangare kuwa, Lai Hongjing, mamba a kwamitin tsare tsare na gasar Cun Chao, kuma mai koyar da ilimin motsa jiki a makarantar sakandare ta 1 ta Rongjiang, gasar Cun Chao ta fadada damammaki ga mutanen kauyuka na ganin duniya, da gina dandalin musaya tsakanin al’ummun sassa daban daban.

DANDALIN KASA DA KASA

Tun bayan kaddamar da gasar, Cun Chao na ta kara fadada tasirin ta tsakanin sassan duniya, tana kuma kara janyo ra’ayin kungiyoyin kwallon kafa na wasu sassan duniya, irin su kungiyar matasa ta Faransa, da ta Liberia, wanda hakan ya haifar da gudanar da wasannin sada zumunta tsakanin ‘yan wasan bangarorin.

A farkon watan Mayu, an gudanar da irin wadannan wasanni tsakanin kungiyar Liberia daga nahiyar Afirka, da takwararta ta Liaoning Donggang ta kasar Sin, wasan da ya gudana a filin gasar VSL.

Moses Barclay, daya ne daga cikin jami’ai dake aiki a ofishin jakadancin kasar Liberia dake Sin, inda ya shafe shekaru 8 yana aiki a ofishin, ya kuma ce al’ummun Rongjiang masu taka leda, da yanayin kauyen su dukkanin su suna da ban sha’awa.

Moses Barclay ya ce "Akwai kasashen nahiyar Afirka masu yawa dake sha’awar buga kwallon kafa. Kuma ta hanyar shirya wasannin kwallo, nahiyar Afirka za ta iya kara dinkewa da Rongjiang, da ma kasar Sin baki daya. Ina fatan karin kungiyoyin kwallon kafar Liberia, ciki har da babbar tawagar kwallon kafa ta kasar, za su samu damar buga wasa a Rongjiang.

Yanzu haka dai an bude gasar VSL ta Afirka irinta ta farko tun a watan Mayu a Parakou na kasar Benin. Kuma mazauna yankunan karkara sun rika zuwa kan babura tare da yaransu domin kallon wasannin gasar.

Shou Xiaoyong, wanda ya fara gabatar da tsarin gasar ta VSL a Afirka, kuma babban kocin Sin dake aiki da kungiyar kwallon kafar ta Benin, ya ce a nan gaba, suna fatan tura kwararrun ‘yan wasa daga kauyuka don taka leda a Guizhou, wato wurin da aka yanke cibiyar gasar kwallon kafa ta kauyuka, domin su fafata da mazauna wurin tare.

A cewar mashirya gasar, za a yi wasannin sada zumunta na Cun Chao tsakanin kasashe dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, a watanni 6 na karshen shekarar nan ta 2024.

Xu Bo, shi ne shugaban gwamnatin gundumar Rongjiang, ya ce Cun Chao ya ja hankalin mazauna kauyen da masu sha’awar kwallon kafa daga dukkanin sassan kasar Sin. A yanzu gundumar na yin aiki tukuru wajen jawo hankalin karin mutane daga dukkanin sassan duniya, ta yadda su ma za su nishadantu daga wasan.

Dong Yongheng, dan wasan VSL ya nanata cewa, "A wannan lokaci, gasar Cun Chao za ta kara yin tasiri, da kara taimakawa wajen bunkasa kawance tsakanin Sin da sauran sassan duniya".