Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin cewa ba zai taba baiwa ’yan Najeriya kunya ba a tsawon mulkinsa
2024-06-13 09:10:10 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa ba zai taba baiwa ’yan kasar kunya ba a iya tsawon shekarun da zai shafe yana mulki.
Ya tabbatar da hakan ne jiya Laraba 12 ga wata a cikin jawabin da ya gabatarwa al’ummar kasar ta kafafen yada labarai a wani bangare na shagulgulan bikin ranar demokradiyya da ake gudanarwa a duk ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya saurari jawabin shugaban ga kuma kadan daga cikin abubuwan da ya tsakuro mana.
Bikin na bana ya zo daidai da lokacin da Najeriya ke cika shekaru 25 kan tafarkin mulkin demokradiyya ba tare da katsewa ba.
Shugaban na tarayyar Najeriya ya yi kira ga daukacin ’yan kasar da su kara nuna juriya a kan irin wahalhalun da suke sha sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki, inda ya ce, matakan da ake bi su ne sahihai da za su dora tattalin arzikin kasar kan ginshiki mai inganci.
“Tattalin arzikinmu yana matukar bukatar garambawul tun shekaru goma da suka gabata domin dai ko kadan babu daidaito a cikinsa sabo da an gina shi bisa tubalin toka, inda aka raja’a kachokan kan kudaden shigar da ake samu daga man fetur, akwai bukatar a fadada zuwa wasu bangarorin tattalin arziki.”
A kan batun ’yan kungiyar kodago kuwa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, ya yaba bisa yadda aka samu damar warware matsalolin da suka taso cikin yanayi na dattako, inda ya ce, yana alfaharin cewa gwamnatinsa ta yi abun da sauran gwamnatoci ba su taba yi ba wajen warware rikicin ’yan kadago ba tare da cin zarafin kowanne ma’aikaci ba.
“Mun cimma shawarwari bisa imani na gaskiya da amana tare da kungiyoyin ma’aikata a kan batun mafi kankantar tsarin albashi na kasa, kuma nan ba da jimawa ba za mu mika kudurin dokar zuwa majalissar kasar da nufin sanya ta cikin wani bangare na kundin dokar kasa na tsawon wa’adin shekaru biyar.” (Garba Abdullahi Bagwai)