Ba za a tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Gaza ba har sai Amurka ta daina samarwa Isra’ila da makamai
2024-06-13 20:29:05 CMG Hausa
DAGA MINA
Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2735 a ran 10 ga watan nan da muke ciki. Inda kudurin ya yi kira da a tabbatar da tsagaita bude wuta tsakanin Palasdinu da Isra’ila a dukkan fannoni nan da nan. A karon farko ne kwamitin ya zartas da irin wannan kuduri, duba da cewa kudurori na wucin gadi da aka gabatar a baya ba su samu amincewa daga bangaren Amurka ba. Sai dai a wannan karo, ‘yan siyasar Amurka sun gabatar da daftarin kudurin, na neman a tsagaita bude wuta a wurin, da nufin kaucewa ci gaba da kawo cikas ga babban zaben dake tafe a kasarsu.
Alal hakika, Amurka ce ke da nauyin samar da gudunmowa ga yunkurin magance rikicin. Da ma sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya gaza cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta a ziyararsa sau da dama a gabas ta tsakiya, sakamakon yadda yake zaune inuwa guda da Isra’ila, da goya mata baya da ma samar mata da makamai.
Zartas da kudurin a wannan karo ya samarwa yankin Gaza damar kawo karshen rikicin. Ana fatan Amurka za ta ba da taimako ga yunkurin tsagaita bude wuta yadda ya kamata, kasancewar ba za a iya warware wannan batu daga tushe ba, har sai Amurka ta dauki matsayin adalci, ta daina samarwa Isra’ila da makamai. (Mai zane da rubutu: MINA)