logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Sin a Niger ya shirya liyafar maraba da sabuwar tawagar jami'an lafiyan Sin a kasar

2024-06-13 10:59:41 CMG Hausa

 

Ofishin jakadancin Sin dake kasar Niger ya gudanar da liyafar maraba da sabuwar tawagar jami’an jinya karo na 24, tare da ban kwana da na 23. Jakadan Sin dake kasar Jiang Feng ya halarci liyafar tare da gabatar da jawabi.

A cikin jawabinsa, Jiang ya ce, tun lokacin da Sin ta fara tura tawaga a karon farko a shekarar 1976, tawagogin sun dukufa wajen tallafawa jama’ar Niger bisa kyawawan fasahohin jiyya, abin da ya sa su kara azama kan sada zumunta tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, jami’an tawagar karo na 23 sun sauke nauyin dake wuyansu, sun kuma kammala ayyukansu yadda ya kamata, yana mai fatan tawagar karo na 24, za ta ci gaba da yayata ruhin tawagar jami’an lafiyan Sin wato rashin jin tsoron shan wahala da kokarin ba da jiyya da ceton mutane da nuna kauna, da daukar matakan da suka dace don kafa kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya a bangaren kiwon lafiya da ba da jiyya. (Amina Xu)