logo

HAUSA

Li Qiang: Ci gaban Sin da New Zealand, dama ce a gare su

2024-06-13 16:24:24 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce ci gaban kasashen Sin da New Zealand, dama ce ga kasashen biyu, maimakon kalubale.

Li Qiang ya bayyana haka ne yau Alhamis, yayin ganawarsa da takwaransa na New Zealand Christopher Luxon, inda ya kara da cewa, ya kamata kasashen biyu su ci gaba da kasancewa abokan hulda masu girmama juna da aminci da moriyar juna da ma koyi da juna, haka kuma abokan hulda masu hadin kai.

Har ila yau, firaministan Sin ya yi kira ga New Zealand da Sin, da su kawar da duk wani tsaiko da ba na tattalin arziki ba a dangantakarsu ta cinikayya da tattalin arziki, ta yadda za su samarwa harkokin kasuwanci kwarin gwiwa da kyakkyawan muhalli.

Ya kara da cewa, Sin na fatan New Zealand za ta mara baya ga yankin Hong Kong ya shiga yarjejeniyar bunkasa tattalin arziki ta Asiya da yankin Pacifik (RCEP). (Fa’iza Mustapha)