logo

HAUSA

Tattalin Arzikin Sin Na Da Karfi Da Kwarin Gwiwar Ci Gaba

2024-06-13 20:12:42 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum a yau Alhamis. Yayin da yake tsokaci game da hasashen babban bankin duniya na karuwar habakar tattalin arzikin Sin a bana, daga kaso 4.5 zuwa 4.8, Lin Jian ya ce akwai hukumomin kasa da kasa da dama da suka yi hasashen habakar tattalin arzikin Sin, wanda hakan ya nuna cikakkiyar amincewar al'ummar duniya da tattalin arzikin Sin. Ya ce cikin yanayin kasa da kasa mai sarkakiya, kuma mai cike da yake-yake da sauye sauye, tattalin arzikin Sin yana da karfi da kwarin gwiwar samun ci gaba.

Game da sanarwar da ma'aikatar kudi ta Amurka ta fitar kwanan nan, cewa za a kakabawa Rasha sabon zagayen takunkumi, Lin Jian ya ce, Sin na adawa da duk wani haramtaccen takunkumi na bangare daya, da amfani da ikon shari'a kan wasu ba tare da bin ka’ida ba. Ya kuma bayyana cewa, game da batun Ukraine, wasu Amurkawa suna furta batun bin ka'idoji da akidu a fatar baki, amma burin su shi ne samun riba da kasuwanci.

Game da bashin kudin karo karo, na dakile sauyin yanayi da ake bin kasashe masu ci gaba, wanda yawansa ya haura dalar Amurka biliyan 300, Lin Jian ya ce, yanayin yana matukar gurgunta kokarin duniya na magance sauyin yanayi.

Sai kuma batun matakin da kwamitin EU ke son aiwatarwa na kara harajin kwastam na wucin gadi kaso 38.1 bisa dari, kan motoci masu amfani da lantarki da ake shigarwa sassan Turai daga kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, EU ta dauki mataki ba tare da la’akari da gaskiya, da ka'idodin cinikayyar kasa da kasa ba, wanda kuma hakan zai haifar da illa ga kowa, ba tare da amfanar su kan su kasashen na Turai ba. Ya ce Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tinkarar hakan. A dai wannan rana, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana cewa, ayyukan EU suna haifar da tarnaki ga hadin gwiwar samun moriya tare tsakanin Sin da Turai a fannin cinikayyar motocin dake amfani da sabbin makamashi.(Safiyah Ma)