logo

HAUSA

PPI na kasar Sin ya ragu da kashi 1.4 cikin dari a watan Mayu

2024-06-12 14:28:53 CMG Hausa

Adadin farashin kayayyaki da masana’antu ke samarwa a kasar Sin (PPI), wanda ke auna farashin kayayyaki daga kofar masana’antu, ya samu raguwa sosai a watan Mayu idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, inda ya ragu da kashi 1.4 cikin dari idan aka kwatanta da raguwar kashi 2.5 cikin dari a wata da ta gabata, kamar yadda bayanan suka nuna a hukumance.

Hukumar Kididdiga ta Kasar Sin (NBS) ta danganta hakan da tashin farashin kayayyaki na duniya da kuma ingantuwar yanayin bukatun kayayyakin masana’antu da ma yadda ake samar da su a kasuwannin cikin gida.

Adadin farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin (CPI), wanda shi ne babban ma'aunin hauhawar farashin kayayyaki, ya karu da kashi 0.3 cikin dari a watan Mayu idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kamar dai yadda bayanan NBS suka nuna. (Yahaya)