logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen kasashen BRICS da na wasu kasashe masu tasowa sun yi tattaunawa

2024-06-12 11:12:44 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron tattaunawa tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen BRICS da na kasashe masu tasowa wato BRICS+, a jiya Talata a birnin Nizhni Novgorod na kasar Rasha. Mambobin kasashen BRICS 10 da wasu muhimman kasashe dake iya wakiltar kasashe masu tasowa 12, ciki har da Thailand da Laos da Vietnam da Bangladesh da kuma Sri Lanka da Kazakhstan, kana da Belarus da Turkey da Mauritania kuma da Cuba da Venezuela da Bahrain, sun yi musayar ra’ayoyinsu kamar yadda ya kamata.

Yayin tattaunawar, Wang Yi ya ce, yanzu ana cikin zamani mai sauye-sauye da rikice-rikice. Rikicin da ya dabaibaye Ukraine da zirin Gaza, da tsaron yanar gizo da sauyin yanayi na kalubalantar duk fadin duniya. Wasu kasashe zaune inuwa guda suke kakkaba takunkumi bisa kashin kai, da sanya shingaye don kare karfin babakerensu, tare da yin amfani da matakan tattalin arziki da hada-hadar kudi a matsayin makamansu na kaiwa saura hare-hare. Matakin da ya habaka gibin dake tsakanin kasashe masu wadata da masu tasowa, kuma ya kawo babbar illa ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Duk da haka, a wani bangare na daban, kasashe masu tasowa na ci gaba da samun bunkasuwa da kyautatuwa. Kasuwanni masu saurin ci gaba da karfi da kasashe masu tasowa suna samun bunkasuwa cikin hadin kai, abin da ya gaggauta habaka ra’ayin mabambantan madogarai.

Kazalika, Wang Yi ya ba da shawarwari guda 3 game da yadda za a bullo da sabbin damammaki cikin sauye-sauyen, wato da farko dai, kiyaye tsaron duniya cikin hadin kai don tinkarar kalubaloli tare. Sannan, mai da samun ci gaba a gaban komai da tattara karfin samun bunkasuwa cikin hadin gwiwa. Daga karshe dai, nacewa kan adalci da daidaito da kyautata tsarin daidaita harkokin duniya. (Amina Xu)