logo

HAUSA

UNICEF ya kafa tsarin gudanar da allurar rigakafi a daruruwan wurare a Libya

2024-06-12 10:38:23 CMG Hausa

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ko UNICEF a takaice ya bayyana a ranar Talata cewa, an kafa tsarin gudanar da allurar rigakafi a wurare 624 a kasar Libya.

UNICEF a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, ya kafa dandalin mai suna Tahseen ne tare da hadin gwiwar cibiyar yaki da cututtuka ta kasar Libya.

“Dandalin na Tahseen na iya bin diddigin yaran da aka yi wa allurar rigakafi, da saukake aikin rajista da adana bayanan matsayin rigakafin. Har ila yau, tsarin ya hada cibiyoyin rigakafin tare da sashen shirye-shiryen allurar rigakafi na kasa, kuma yana ba da cikakkun rahotanni don sa ido da kuma bincike," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa, UNICEF ya sanya tsarin kula da yanayin zafi a dakunan ajiyar allurar rigakafi 94 na kananan hukumomi don tabbatar da adana alluran a yanayi mafi kyau. (Yahaya)