logo

HAUSA

Xi ya gabatar da jawabin bude taron cika shekaru 60 da kafuwar UNCTAD ta kafar bidiyo

2024-06-12 21:24:23 CMG Hausa

A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin bude taron cika shekaru 60 da kafuwar dandalin MDD na tattauna harkokin cinikayya da samar da ci gaba ko UNCTAD a takaice ta kafar bidiyo.

Cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya yi kira ga dandalin da ya kara azamar samar da kyakkyawan muhallin kasa da kasa, na zaman lafiya da ci gaba, ya kuma rungumi tafarkin bunkasuwa, da amfani da damammakin tarihi na ci gaban kirkire kirkire.

Ya ce Sin za ta shiga a dama da ita, wajen fadada shigo da hajoji daga sauran kasashe masu tasowa, da karfafa cinikayya, da zuba jari, da bunkasa hadin gwiwa, da taimakawa wajen aiwatar da ajandar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD, ko SDGs ta nan zuwa shekarar 2030. (Saminu Alhassan)