logo

HAUSA

Jita-jitar Amurka game da wai Sin na samun koma baya ba ta da tushe ko kamaka

2024-06-12 07:48:29 CMG Hausa

’Yan siyasar Amurka sun shafe tsawon lokaci suna yada jita-jita iri iri game da kasar Sin, a wani mataki na farfagandar neman samun fifiko, da takara maras amfani, wadda ba ta haifar da komai sai koma baya ga dangantakar sassan biyu, da haifar da zaman doya da manya tsakanin Sin da Amurka.

Mun ji yadda a makwannin baya, Amurka ta bullo da batun bincikar ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin dake shiga Amurka, wadanda ’yan siyasarar Amurkan suka zargi cewa, suna iya zama barazanar tsaron kasa, da ma kare-karen haraji da gwamnatin Amurka ta rika dorawa kan hajojin da ake shigarwa daga Sin zuwa sassan kasar, lamarin da ya illata moriyar ’yan kasuwa, da Amurkawa masu sayayya, kana ya dagula tsarin rarraba hajoji a sassan kasa da kasa.

Wani abun damuwa shi ne yadda ’yan siyasar Amurka ke kallon duk wani ci gaba da kasar Sin ta samu a matsayin babbar barazana ga kasarsu. Suna fakewa da batutuwa daban daban, domin tabbatar da aniyarsu ta nuna gazawar Sin, ko koma bayan da suke cewa kasar za ta samu.

To sai dai kuma, duk wasu kalubale da wadannan ’yan siyasa na Amurka ke lasaftawa a matsayin dalilansu, muna iya kallonsu a matsayin kalubaloli dake wakana a dukkanin sassan duniya. Bugu da kari, wadannan ’yan siyasa masu kitsa zarge-zarge game da kasar Sin, ba sa tabo sassan da kasar Sin din ke cimma nasarori a cikinsu, musamman fannin ingancin manufofin bunkasa kasa, da kyautatuwar zamantakewar al’umma, da yadda gwamnatoci a dukkanin matakai ke tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da sauye-sauye, da bunkasa tattalin arzikin kasar ta Sin.

A baya bayan nan, yayin wata zantawa da mujallar “Times”, an jiyo shugaban Amurka Joe Biden na cewa a hasashensa, wai tattalin arzikin kasar Sin na kan gabar durkushewa. To sai dai kuma wannan hasashe nasa, na zuwa ne a gabar da asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya daga hasashensa game da bunkasar mizanin awon tattalin arzikin Sin ko GDP, da kaso 5 bisa dari a bana, adadin da ya haura wanda asusun ya yi a watan Afirilu.

Ko shakka babu, kasar Sin ta samu bunkasuwa a fannonin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da sarrafa makamashi masu tsafta, da kirar ababen hawa masu aiki da lantarki, da raya fannin fasahar kirkirarriyar basira ko AI. A daya bangaren, kasar ta samu ci gaba mai armashi a fannonin raya masana’antu daban daban bisa kwazo da sanin makamar aiki.

Alamu sun shaida cewa, ’yan siyasar Amurka, da ’yan korensu na kasashen yamma, sun shiga rudadi, idon su ya rufe game da duk wani ci gaba da Sin ke samu, don haka, suka shiga kitsa zarge-zarge, da karairayi da nufin shafawa kasar kashin kaji, da yunkurin mayar da kasar baya, ta hanyar yi mata mummunan fata ba tare da wasu sahihan hujjoji ba. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)