logo

HAUSA

Hamas ta mai da martani kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta

2024-06-12 11:07:44 CMG Hausa

 

Hamas da Jihad sun ba da wata hadaddiyar sanarwa a jiya Talata cewa, sun bayyana wa Qatar da Masar, wadanda suke shiga tsakanin rikicin Palsdinu da Isra’ila, matsayinsu game da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Wannan sanarwar ta mai da moriyar Palasdinawa a gaban komai, a ganinta, ya kamata Isra’ila ta daina bude wuta a zirin Gaza daga dukkan fannoni tare da janye jikinta daga yankin. Wakilin Palasdinawa na fatan sauke nauyin dake wuyansu, don kai ga matsaya daya kan yarjejeniyar don kawo karshen yaki dake kai hari kan jama’a.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta ba da wata sanarwa a daren wannan rana cewa, Qatar da Masar sun san ra’ayin Hamas kan yarjejeniyar. Suna hadin kai da Amurka wajen kokarin sulhuntawa, da daukar matakan da suka dace da bangarori masu ruwa da tsaki nan gaba.

Kafofin yada labarai na Isra’ila sun ruwaito jawabin wani babban jami’in kasar cewa, Isra’ila ta samu martanin da Hamas ta yi game da yarjejeniyar, amma Hamas ta yi babbar gyara, hakan ya kasance abin takaici. (Amina Xu)