Xi ya ba da amsa ga wasikar farfesan Tsinghua, inda ya bukaci karin gudummawa ga ilimi da kimiyya
2024-06-12 14:23:57 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafa gwiwar Andrew Chi-Chih Yao, farfesa a jami’ar Tsinghua, da ya kara ba da gudummawarsa ga horar da kwararru da kirkire-kirkiren kimiyya na kasar.
Xi ya bayyana hakan ne a cikin wata amsar wasikar da ya aike wa Yao, masani na cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin da ya dawo kasar Sin, kuma ya fara aikin koyarwa a jami’ar Tsinghua shekaru 20 da suka gabata. (Yahaya)