logo

HAUSA

Ka’idar “Kasar Sin daya tak a duniya” tushen huldar kasa da kasa da al’ummar duniya ke amincewa da ita

2024-06-12 11:27:48 CMG Hausa

 Da safiyar yau ne ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira taron manema labarai. Inda mai magana da yawun ofishin Chen Binhua ya nuna cewa, batun Taiwan harka ce na cikin gidan kasar Sin, ba wanda ya isa ya tsoma baki. Ka’idar “Kasar Sin daya tak a duniya” tushen huldar kasa da kasa kuma al’ummar duniya sun amince da ita. Sin na yabawa matsayin da al’ummar duniya suke dauka, na fahimta da goyon bayan sha’anin Sin na yaki da ware yankin daga gare ta da neman samun cikakken yankinta.

Ban da wannan kuma, Chen Binhua ya ce, Taiwan wani yanki ne da ba za a iya ware shi daga kasar Sin ba, tarihi ya shaida hakan kuma wasu dokoki na shari’a a duniya sun tabbatar da hakan. Masu kawo baraka da masu tsoma baki su ne suke tayar da hankali a yankin.

Lai Ching-te da jam’iyyarsa sun kalubalanci wannan ka’ida da rura wuta wajen tada rikici tsakanin babban yanki da shi, da zummar ware yankin bisa dogaro da karfin kasashen waje da karfin tuwo, abin da ya sabawa ra’ayin jama’a a yankin, kuma ya keta zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin, bala’i kawai zai kawowa jama’ar yankin. (Amina Xu)