logo

HAUSA

Shugaban AU da na MDD sun mika ta’aziyyarsu kan rasuwar mataimakin shugaban kasar Malawi da wasu mutane tara

2024-06-12 10:12:09 CMG Hausa

A jiya Talata ne shugaban hukumar tarayyar Afirka wato AU Moussa Faki Mahamat ya mika ta’aziyyarsa kan rasuwar mataimakin shugaban kasar Malawi da wasu mutane tara.

An tabbatar da rasuwar mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Chilima da wasu mutane tara da ke cikin wani jirgin saman soji, bayan da jirgin ya yi batar dabo da safiyar ranar Litinin, kamar yadda shugaban kasar Lazarus Chakwera ya bayyana a jiya Talata.

Faki ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu, da gwamnati da al’ummar Malawi kan wannan babban rashi na kasa. Faki ya nanata cikakken goyon bayan AU ga Chakwera, gwamnati da al'ummar Malawi a wannan mawuyacin lokaci.

A daya bangare kuma, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bakin cikinsa kan hatsarin jirgin saman da ya faru a ranar Litinin, wanda ya hallaka mataimakin shugaban kasar Malawi da wasu mutane tara, a cewar mataimakin kakakinsa a ranar Talata. (Yahaya)