Sin ta mika sakon ta'azziyar rasuwar mataimakin shugaban Malawi
2024-06-12 19:32:53 CMG Hausa
Yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa.
Game da rasuwar mataimakin shugaban kasar Malawi Saulos Chilima, sakamakon hadarin jirgin sama, Lin Jian ya ce, bangaren Sin ya gabatar da ta’azziyar rasuwarsa, da sauran mutanen da hadarin jirgin ya rutsa da su, tare da jajantawa iyalansu.
Game da takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin Sin guda uku, bisa hujjar wai suna “Tilastawa al’ummar kabilar Uygur yin ayyukan kwadago”, Lin Jian ya ce, bangaren Amurka ya sake tsarawa, da kuma yada labarai marasa tushe game da jihar Xinjiang, ya kakaba takunkumi ga kamfanonin Sin ba tare da bin dokoki ba, ta fakewa da batun “hakkin bil’adama”. Bangaren Sin yana matukar adawa da hakan, kuma ya yi Allah wadai da matakin.
Game da batun yadda Amurka ke yunkurin kara dakile Sin, ta fannin samun fasahar kananan na'urorin lantarki da ake amfani da su a ayyukan fasahar AI, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin Amurka ba zai hana ci gaban kimiyya da fasahar Sin ba, maimakon hakan zai baiwa kamfanonin Sin din kwarin gwiwa ne na dogaro da kan su.
Sai kuma batun shirin kungiyar tarayyar Turai ta EU, na kara kudin kwastan ga motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, inda Lin Jian ya ce, bangaren Sin zai dauki dukkan matakan da suka dace, don kiyaye iko da moriyarsa.(Safiyah Ma)