logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci taron ministocin BRICS

2024-06-11 11:44:46 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin kungiyar BRICS a jiya Litinin a birnin Nizhni Novgorod na kasar Rasha.

Yayin taron, Wang Yi ya ce, hadin gwiwar kasashen BRICS ya gudana cikin sauri da inganci a cikin shekara daya da ta gabata, inda har BRICS ta shigar da sabbin mambobi, matakin da ya bude sabon babin hadin gwiwar kasashe masu tasowa dake dogaro da karfinsu, abin da ya sa BRICS ke kara jan hankalin duniya.

Wang Yi ya ce, “dole ne mu nace ga tabbatar da adalci da gaskiya, mu bi hanyar da ta dace da yanke shawara yadda ya kamata, duba da cewa ana fuskantar ja-in-ja tsakanin ra’ayin mu’amalar bangarori daban daban a duniya da na babakere, da ma ra’ayin bangarori da na kashin kai.”

Ya kara da cewa ya kamata a yi amfani da tsare-tsare da tasirin siyasar kungiyar yadda ya kamata don mai da BRICS wani sabon tsari mai yakini na hadin kan kasa da kasa da bude kofa dake dogaro da tushen kasuwanni masu saurin ci gaba da karfin kasashe masu tasowa.

Mahalarta taron sun yabawa babban tasiri da ci gaban shigar da sabbin mambobi da BRICS ya samu, inda suke ganin cewa, shigar da karin mambobi cikin kungiyar za ta gaggauta samar da iko tsakanin bangarori da dama a duniya da ingiza doka da odar kasa da kasa mai adalci da daidaito, kuma sun amince da tsarin shigar da kasashen hulda cikin kungiyar, inda kuma aka gabatar da “Hadaddiyar Sanarwa Game Da Ganawar Ministocin Wajen Kasashen BRICS”.

Yayin taron, Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov da na Brazil Mauro Vieira da na Habasha Taye Atske-Selasie da sauransu. (Amina Xu)