logo

HAUSA

Jirgin da ya tashi dauke da mataimakin shugaban Malawi ya fadi tare da hallaka dukkanin mutane dake cikin sa

2024-06-11 19:59:15 CMG Hausa

A yau Talata, shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera, ya ce masu aikin ceto sun gano sassan jirgin nan da ya tashi dauke da mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima, da wasu jami’an gwamnati a kusa da wani tsauni. Shugaba Chakwera ya ce jirgin ya yi hadari, kuma dukkanin mutane dake cikin sa sun rasu, ciki har da mataimakin shugaban kasar.  (Saminu Alhassan)