logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki matakan kawo karshen safarar kananan ’yan mata zuwa kasashen waje

2024-06-11 10:06:59 CMG Hausa

Ministan harkokin ci gaban mata ta tarayyar Najeriya Mrs Uju Kennedy-Ohanenye ta tabbatar da cewa, gwamnati ta fara daukar tsauraran matakai da za su kawo karshen safarar kananan ’yan mata zuwa kasashen wajen domin gudanar da haramtacciyar sana’ar karuwanci.

Ministan ta tabbatar da hakan ne ranar Litinin 10 ga wata lokacin da ta ziyarci ofishin jakadancin Ghana dake birnin Abuja domin bibiyar yadda aka yi safarar wasu kananan ’yan mata zuwa kasar Ghana tare kuma da tattauna yadda za a maido da su gida Najeriya, ministan ta ce, daga cikin matakan akwai hukunci mai tsanani ga dillalai da kuma su kansu iyayen yaran.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ziyartar ofishin jakadancin dai ya biyo bayan hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta, inda ake nuna yadda aka yi safarar wasu kananan ’yan matan Najeriya zuwa kasar Ghana, kuma aka tilasta musu aikata karuwanci.

“Abu na farko da na fara yi shi ne zuwa ofishin jakadancin kasar Ghana saboda akwai bukatar mu yi aiki tare domin duba hanyoyin da za mu dawo da wadannan ’yan mata gida.”

Daga ofishin jakadancin ne kuma ministan matan ta tarayyar Najeriya ta zarce zuwa ofishin hukumar yaki da safarar bil’adama ta Najeriya inda ta gudanar da ganawar sirri da darakta janaral ta hukumar farfesa Fatima Waziri-Azi, bayan sun kammala ganawar ne, darakta janaral din ta yi wa manema labarai karin haske a game da matakin da ake kai a yanzu.

“Muna magana da sashen kula da harkokin safarar bil’adama na kasar Ghana, kuma an tabbatar mana cewa an samu ceto yaran, kuma an killace su, haka kuma an kama wadanda suka aikata wannan laifi.”

Adadin kananan ’yan mata 10 ne dai aka yi safarar tasu zuwa kasar ta Ghana domin aikata mummunar sana’ar karuwanci wanda yanzu haka kuma shirye-shirye sun yi nisa wajen dawo da su Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)