logo

HAUSA

UNESCO: Mu’ammala tsakanin mabambantan al’adu na da muhimmanci wajen samun makoma mai dorewa

2024-06-11 14:45:14 CMG Hausa

 

Mai ba da taimako ga babbar darektar hukumar kula da ba da ilmi da kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO madam Gabriela Ramos ta yi maraba da yadda babban taron MDD ya zartas da kudurin da kasar Sin ta gabatar na ayyana ranar tattaunawa tsakanin mabambantan al’adu, inda ta jaddada cewa, yin tattaunawa tsakanin mabambantan al’adu na da muhimminci sosai ga samun makoma mai dorewa.

Ramos ta ce, ayyana irin wannan rana zarafi ne wajen bullo da boyayyen karfin mu’ammla, wanda zai zama wata kyakkyawar gada, duk da kasancewar bambancin ra’ayi, ta yadda za a samar da hanyoyi masu dacewa wajen daidaita duk wata matsala.

A ran 7 ga watan nan, babban taron MDD karo na 78 ya zartas da kudurin da Sin ta gabatar na ware ranar mu’ammala tsakanin mabambantan al’adu, inda aka ayyana ranar 10 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin wannan rana. (Amina Xu)