logo

HAUSA

Xi ya sanya hannu kan dokar aiwatar da ka’idojin tantance ayyukan kasafin soji

2024-06-11 19:29:37 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin, kuma jagoran hukumar zartaswa ta rundunar sojojin kasar Xi Jinping, ya sanya hannu kan dokar aiwatar da ka’idojin da aka yi bitar su, don gane da tantance ayyukan kasafin soji.

Ka’idojin dai sun fayyace a fili, irin matakan da za a aiwatar a fannin tantanci hada hadar tattalin arziki mai nasaba da kasafin rundunar sojojin kasar, tare da jaddada yanayi, da ayyukan siyasa masu nasaba da wannan muhimmin aiki. Kaza lika ka’idojin sun tanadi karin dokoki da za a rika kiyayewa, yayin da ake gudanar da aiki mai nasaba da hakan. (Saminu Alhassan)