logo

HAUSA

Kasar Sin za ta zurfafa kawance da hadin gwiwa da Habasha

2024-06-11 11:17:08 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce a shirye kasarsa take ta zurfafa abota da fadada hadin gwiwa a bangarori daban daban da kasar Habasha.

Wang Yi ya bayyana haka ne jiya Litinin a ganawarsa da takwaransa na Habasha, Taye Atske Selassie, a birnin Nizhny Novgorod na kasar Rasha.

Da yake bayyana Habasha a matsayin muhimmiyar kasa a nahiyar Afrika, kuma mai masaukin hedkwatar kungiyar Tarayyar Afrika (AU), Wang Yi ya ce, zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar na da muhimmanci ga nahiyar. Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta zurfafa abota cikin kowanne yanayi, da fadada hadin gwiwa a bangarori daban daban, da kuma ingiza samun karin nasarori a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, domin jama’arsu su amfana da su.

A nasa bangare, Taye Atske Selassie ya ce, gwamnati da al’ummar Habasha na maraba da daukaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa ta abota bisa manyan tsare-tsare a kowanne yanayi. Ya kara da cewa, kasar Sin ce babbar mai zuba jari a Habasha, haka kuma inda ta fi shigar da kayayyakinta, kana dangantakar dake tsakaninsu ta bunkasa tattalin arziki da kyautata zamantakewar Habasha.

Bugu da kari, ya ce a shirye Habasha take ta yi koyi da hanyoyin da Sin ta bi wajen samun ci gaba, da kuma kara inganta hadin gwiwar Sin da Afrika, tare da sauran kasashen nahiyar. (Fa’iza Mustapha)