logo

HAUSA

Kasashen Afrika na kira da a gaggauta yi wa Kwamitin Sulhu na MDD garambawul

2024-06-11 13:03:16 CMG Hausa

Kwamishinan kula da harkokin siyasa da tsaro da zaman lafiya na Tarayyar Afrika (AU), Bankole Adeoye ya nanata bukatar yi wa kwamitin sulhu na MDD garambawul, yana mai kira da tattaunawa tsakanin kasashen Afrika domin gaggauta hakan.

Kamfanin dillancin labarai na Algeria APS, ya ruwaito Bankole Adeoye na bayyana haka ne jiya Litinin a birnin Algiers na Algeria, yayin wani taron ministoci karo na 11 na kwamitin AU mai shugabannin kasashe da gwamnatoci 10 game da yi wa kwamitin sulhu na MDD garambawul. Bankole Adeoye ya kuma bayyana wasu batutuwa da suka wajaba a aiwatar da su a nahiyar, wadanda suke da wajibcin kawar da makamai da yaki da ta’addanci da cimma dunkulewar nahiyar da tabbatar da kyautata wakilcin nahiyar a duniya.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen Algeria Ahmed Attaf ya ce, nahiyar Afrika na son a yi wa kwamitin sulhun garambawul, ta yadda za a kawar da rashin adalcin da aka dade ana yi da nisanta shi daga takkadama da rarrabuwar da suke tarnaki ga aikinsa. Yana mai jaddada cewa, wariyar da ake nuna wa Afrika a kwamitin, yana mummunan tasiri ga tsarin harkokin duniya baki daya.

Shi kuwa Timothy Musa Kabba, ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Saliyo, wanda kasarsa ke shugabantar wancan kwamiti na AU, ya bayyana wajibcin cimma matsaya tsakanin kasashen Afrika game da yi wa kwamitin sulhun garambawul. Yana mai kira ga shugabannin kasashen su gaggauta tattaunawar da za ta kai ga cimma wannan manufa.

Kwamitin wanda aka kafa a 2005, ya kunshi kasashen Algeria da Congo da Equatorial Guinea da Kenya da Libya da Namibia da Saliyo da Senegal da Uganda da kuma Zambia. (Fa’iza Mustapha)