Kara mu’amala tsakanin mabambantan al’ummomin duniya zai kawar da sabani da rashin fahimta
2024-06-11 18:30:08 CMG Hausa
A duniyar yanzu, babbar matsalar dake haifar da tashe-tashen hankula da rashin girmama juna ita ce, rashin fahimta da mu’amala tsakanin mabambantan al’ummomi. Matukar ana son yi wa tufkar hanci tare da samun duniya mai fahimta da zaman lafiya, sai an inganta mu’amala tsakanin mabambantan al’ummomin duniya.
A karshen makon da ya gabata ne, yayin zaman babban zauren MDD na 78, daukacin mambobin majalisar suka amince da kudurin da Sin ta gabatar na ware wata rana, domin inganta mu’amala da tattaunawa tsakanin mabambantan al’ummomin duniya, inda aka ayyana ranar 10 ga watan Yunin kowacce shekara ta kasance wannan rana.
Hakika hangen nesa irin na kasar Sin ya cancanci yabo. Har kullum cikin bangarorin da take mayar da hankali kansu a hadin gwiwarta da kasa da kasa shi ne, inganta mu’amala da musaya tsakanin al’ummomi, da zummar kyautata fahimta da koyi da juna. Misali, a baya-bayan nan, an yi taron musaya tsakanin matasan Sin da Afrika a birnin Beijing, kuma wannan wani taro ne da kasar Sin kan dauki nauyinsa a kowacce shekara. Ba wannan kadai ba, a ko da yaushe kasar Sin na samar da tallafin karatu ga matasan kasashen duniya daban-daban, domin su zo kasar su yi karatu da mu’amala da takwarorinsu da kuma kara fahimtar al’adu da yanayin kasar, da zummar kawar da sabani da bahaguwar fahimta. Idan zan bada misali da kai na, tabbas ra’ayi da tunanina game da kasar Sin sun sauya bayan zuwana kasar tare da mu’amala da jama’arta, ke nan, lallai mu’amala da cudanya na kara wayar da kan jama’a da samar da fahimtar juna.
Har ila yau a gainina, bambancin al’ada ko addini ko launin fata dake akwai tsakanin al’ummomin duniya, abun alfahari ne ga dan adam, sannan wata dama ce ta karin ilimi. Kowacce al’ada ko kabila na da nata sigogi na musamman, kuma ta hanyar mu’amala da musaya ne kadai, mabambantan al’ummomi za su iya fahimta da hakuri da girmama juna da kuma samun jituwa. Lamarin da zai kai ga samun zaman lafiya da girmama juna, wanda shi ne burin kasar Sin a ko da yaushe.
Dukkan bil adama matsayi daya gare su, babu wanda ya fi wani. Gane darajar dan adam da hakuri da girmama juna ba zai samu ba, har sai an fahimci juna an kuma ma’amalantu. Fatan ita ce, wannan rana da aka ayyana ta taka rawar gani wajen kawo zaman lafiya da dunkulewar al’ummun duniya cikin kwanciyar hankali da lumana. (Faeza Mustapha)